Somaliya

An aiwatar da hukuncin kisa kan sojojin Somaliya biyu

©Reuters/Feisal Omar

GWAMNATIN Kasar Somalia, ta aiwatar da hukucin kisa, kan sojojin ta biyu, da aka samu da laifin kashe wani farin hula, da soja guda.Mai shari’a Hassan Hussein Muungaab, yace sun kama sojin ne yayin da suke aikata laifin, saboda haka suka aiwatar musu da hukunci kamar yadda shari’ar Islama ta tanada.Mutane da dama ne suka kalli aiwatar da kisan, lokacin da sojoji 15 suka bude musu wuta.