Saudiya

Saudiyya ta bayar da tallafi ga Somaliya

Sarki Abdallah na Saudiyya da Sakatariyar wajen Amurka Hillary Clinton
Sarki Abdallah na Saudiyya da Sakatariyar wajen Amurka Hillary Clinton

HUKUMAR Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, tace kasar Saudi Arabia ta bada tallafin Dala miliyan 50 ga kasar Somalia, mai fama da matsalar yunwa.Babban Daraktan Hukumar, Jossette Sheran ya bayyana haka, inda yake cewa, za suyi anfani da kudin wajen ciyar da rabin yaran Somalia dake fama da rashin abinci mai gina jiki.