Najeriya

Tashin Bom a Abuja Hedikwatar Majalisar Dunkin Duniya

Gawawwakin wasu da ake ta kokarin Fitowa da su a Ginin Majalisar Dunkin Duniya a Abuja
Gawawwakin wasu da ake ta kokarin Fitowa da su a Ginin Majalisar Dunkin Duniya a Abuja RFI Hausa

Wani bom ya tashi a ginin Hedikwatar Majalisar Dunkin Duniya a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya. Sai dai har yanzu ba tantance wadanda suka mutu ba sanadiyar tashin Bom din.A yanzu haka dai ‘Yan sandan Najeriya sun kewaye harabar ginin na Mjalisar Dunkin Duniya inda Bom din ya tashi.Wakilin Sashen Hausa na Rfi yace Tun bayan tashin Bom din ne ake ta fito da gawawwaki wadanda suka rasa rayukansu a ginin na Majalisar Dunkin Duniya da al’amarin ya faru.Sai dai kuma kungiyar Boko Haram ta shaidawa Rediyo Faransa daukar nauyin kai harin.