Libya

‘Yan Tawayen Libya sun bukaci kudi daga Asusun libya da aka rufe

'Yan Tawayen Libya a lokacin da suke shirin tunkarar dakarun Gaddafi a Misrata.
'Yan Tawayen Libya a lokacin da suke shirin tunkarar dakarun Gaddafi a Misrata. Reuters/Zohra Bensemra

Mahmud Jibril mataimakin shugaban sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Libya ya yi kira ga kasashen yammaci domin sakin kudaden kasar baki daya da aka rufe, domin samun damar tafiyar da sabuwar gwamnatin dake kokarin ganin karshen shugaban Muammar Gaddafi.A cewarsa akwai bukatu da dama da zasu iya biyowa bayan karya gwamnatin Gaddafi. Don haka ya zama dole a saki kudaden Libya domin girka sabuwar gwamnati da ci gabanta.Tuni dai Majalisar Dunkin Duniya ta saki kudin Libya dala Biliyan 1.5 da aka rufe na asusun kasar.A yanzu haka dai ‘Yan Tawayen su mayar da Hedikwatarsu a Tripoli daga tsohuwar Hedikwatarsu Benghazi. Kuma sun bayyana cewa nan bada jimawa bane shugabansu Mustapha Abdel Jalil zai isa Tripoli idan har aka tabbatar da halin tsaro a babban birnin kasar.