South Sudan

Shugaban Kudancin ya nada sabbin Ministoci

Shugaba yankin Kudancin Sudan Salva Kirr
Shugaba yankin Kudancin Sudan Salva Kirr Reuters

Shugaban kudancin Sudan Siva Kirr a yau Assabar ya nada sabbin Ministoci a kasar, bayan sauya gwamnatin rikon kwarya wacce ta dauki alhakin kula da lamurran gwamnatin tun bayan samun ‘yancin kai a watan jiya.Sabbin Ministocin dai sun hada da Ministan Kudi da Ministan harakokin waje da kuma Ministan kula da albarkatun kasa.A 9 ga watan Juli ne dai kudancin sudan ya samu ;yancin kai bayan ya balle daga arewaci a dukulalliyar Sudan.