LIBIYA-ALJERIYA

WAKALA GADDAFI YAA GUDU ZUWA ALGERIYA

Moamer GaddafI
Moamer GaddafI Wikipedia/profile

Rahotannin da ke fitowa daga kasar ta Algeria na cewa wasu motocin yaki da ake tsammanin suna dauke da manyan jami’an gwamnatin kasar Libya, sun ketare zuwa kasar daga Libya mai makwabta da ita. Rahotannin sun nuna cewa watakila har da shugaba Muammar Gaddafi a cikin wannan tawaggar, sai dai jama’an kasashen 2 sun ki cewa uffan kan lamarin.An dai rasa inda Shugaba Gaddafi ya shiga, tun bayan da babban birnin kasar, Tripoli ya fada hannun ‘yan tawayen da suka shafe watanni 6 suna fafatawa da gwamntin da ya shjekara 42 yana jagoranta.