Libya

‘Yan Tawayen Libya sun karbe ikon Tripoli

'Yan Tawayen Libya a lokacin da suke shirin tunkarar dakarun Gaddafi a Misrata.
'Yan Tawayen Libya a lokacin da suke shirin tunkarar dakarun Gaddafi a Misrata. Reuters/Anis Mili

A yanzu haka ‘yan Tawayen libya sun karbe ikon Birnin Turabulus, musamman yankunan da ke karkashin ikon shugaba Muammar Gaddafi.‘Yan Tawayen sun karbe ikon filin saukar jirgin sama da kan iyakar kasar Libya da Tunisia. Sai dai Tun bayan da ‘yan tawayen suka karbe ikon wasu yankunan Birnin, na turabulus, aka fara shiga matsalar ruwan sha data wutar Lantarki.Har yanzu dai shugaban ‘yan Tawayen yana Benghazi, har sai ‘yan Tawayen sun tabbtar da karbe ikon Turabulus ne shugabanm zai dawo da fadarsa.