Libya-Algeria

Iyalan Gaddafi Sun tsere zuwa Aljeriya

Sofiya Uwargidan Shugaban Libya Muammar Gaddafi tare da 'yayanta
Sofiya Uwargidan Shugaban Libya Muammar Gaddafi tare da 'yayanta

Gwamnatin Algeria ta tabbatar cewa, uwargidan Kanar Gaddafi, Sahiya, da ukku daga cikin 'ya'yansa, sun isa kasar bayan sun tsere daga Libiya.Rehotanni kuma daga Libyan na cewa Kanal Gaddafi da ‘yayansa guda biyu sun buya ne a wani garin Bani Walid dake kudu da birnin Tripoli babban birnin kasar.A daya bangaren kuma dan kanal Gaddafi Khamis inda dadewa aka sanar da cewa ya mutu, daya daga cikin Ministocin ‘yan Tawayen yace an kashe Khamis tare da binne gawarsa a kudancin Tripoli.