Nigeria

Sarkin Musulmi ya la’anci harin ginin MDD a Abuja

Sarkin Musulmin Nigeria Alh. Abubakar Sa'ad 111
Sarkin Musulmin Nigeria Alh. Abubakar Sa'ad 111 Reuters

A Sakonsa ga al’ummar musulmin Nigeria bayan kammala azumin watan Ramadan Sarkin Musulmi Alh Abubakar Sa’ad ya yi tir da Allah waddai da harin da aka kai a ginin Majalisar Dunkin Duniya, abunda ya kira abun la’anta ga addinin Islama.Sarkin Musulmin ya yi kira ga wadanda ke da alhakin kai harin da su amince da matakin sasantawa tsakaninsu da gwamnati a maimaikon kai hare hare da ke lakume rayukan bayin Allah da basu ji basu gani ba.A ranar Juma’ar makon jiya ne dai aka kai harin bom a ginin Majalisar Dunkin Duniya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23. Sai dai kuma kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai harin bayan da kuma jami’an tsaro a Nigeria suke zargin kungiyar Al Qaeda, al’amarin da yasa Majalisar Dunkin Duniya tace zata gudanar da bincike.