Libya

‘Yan Tawaye na bukin Sallah da karya Gaddafi a Libya

Daruruwan 'yan  kasar Libya
Daruruwan 'yan kasar Libya Reuters

Bayan kammala Azumin watan Ramadan, a yau Laraba ne ‘Yan Tawayen Libya ke gunadar da bukukuwan Sallah tare da bukin karya Gwamnatin Gaddafi duk da cewa da sauran rina a Kaba.Daruruwan mutane ne suka taru a wani dandali da suke kira “Dandalin juyayi” domin gudanar da Sallar Eid El Fitr bayan kammala azumin watan Ramadan.Da safiyar yau ne kuma kungiyar kawancen NATO ta tarwatsa wasu yankunan mahaifar Gaddafi birnin Sirte da bama bamai da wani gari da ke kusa da birnin Bani Walid inda ‘Yan Tawayen ke hasashen mabuyar Ghaddafi.