Zambiya-Malawi

Sata ya yi watsi da gayyatar Mutharika na Malawi

Michael Sata Sabon shugaban kasar Zambiya
Michael Sata Sabon shugaban kasar Zambiya @Reuters

Shugaban Kasar Zambiya, Michael Sata, ya ki amincewa da gayyatar shugaban kasar Malawi, Bingu Wa-Mutharika, na halartar taron kasashen da ke Yankin Sahel, saboda yadda Gwamnati Malawi ta bayyana shi a matsayin bakin haure lokacin da yake adawa.Sata yace, ba zai je Malawi ba, sai Gwamnatin kasar ta nemi gafara, abinda Gwamnatin Mutharika tace ba zata yi ba.