Masar

Shugabannin Addini zasu gana don magance rikicin Masar

Rikicin kasar Masar
Rikicin kasar Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Malaman addini Islama a kasar Masar sun yi kiran taron gaggawa tsakanin shugabannin musulmi da Kirista, bayan barkewar wani mummunan rikici da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 24 tun bayan hambarar da Hosni Mubarak. Shugaban Sunni Shehin Malami Al-Azhar Ahmed al-Tayyeb, ne ya yi wannan kiran a kafar Telebijin din kasar.Wannan kiran na Tayyib na zuwa ne sa’o’I kalilan bayan barkewar rikicin addini tsakanin musulmi da Kirista a birnin Alkahira rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 24 tare da raunata wasu da dama.Tuni dai Gwamnatin Kasar  ta sanya dokar hana fitar dare a birnin Alkahira, sakamakon  taho mugamar da aka yi tsakanin mabiya addinin Krista da jami’an tsaro a karshen mako.