Libya

‘Yan Tawayen Libya sun fara farautar Gaddafi gida-gida a Sirte

Kofar Shiga Jami'ar birnin Sirte ta kasar Libya
Kofar Shiga Jami'ar birnin Sirte ta kasar Libya Reuters

‘Yan Tawayen Libya na ci gaba da farautar Gaddafi a mahaifarsa Birnin Sirte inda a yau Talata suka fara bi gida-gida domin gano maboyarsa.Sai dai kuma masu dakarun Gaddafi na ci gaba da kai wa ‘yan Tawayen hari a yankin Bani Walid, inda suka kashe dakarun sabuwar gwamnatin ‘Yan Tawayen 17.Yanzu haka dai Birnin Sirte ne ya rage wa ‘Yan Tawayen su bayyana mallake kasar Libya wanda hakan zai basu damar samar da jadawalin zabe a cikin kasar.Kwamandan Dakarun ‘Yan Tawayen a Birnin Sirte Wissam Bin Ahmed yace suna gab da karbe ikon birnin Sirte amma har yanzu suna tsoron kare rayuwar fararen hula da ke ci gaba da yin kaura daga birnin.