Amurka-Najeriya

Mutallab ya amsa laifin zarginsa

Umar Farouk Abdulmutallab dauke da bindiga
Umar Farouk Abdulmutallab dauke da bindiga AFP PHOTO/ABC NEWS/HANDOUT

Dan Najeriya da aka zarga da yunkurin tarwatsa jirgin saman Amurka, a shekarar 2009, Umar Faruk Abdulmutallab, ya amsa laifin zargin da ake ma shi. Yace ya yi yunkurin haka ne domin daukar fansar kisan al’ummar musulmi.Yayin da ya ke jawabi a gaban kotu, Abdulmutallab ya bai wa mutanen da ke kotun mamaki wajen amsa laifinsa, inda ya ke cewa a dokar Amurka ya yi laifi, amma a Qur’ani bai yi ba, inda ya kara da cewa, idan yau an masu dariya, gobe mu zamu yi muku dariya.Mutallab ya yi gargadin cewa Amurka zata fuskanci bala’I daga hannun masu jahadi idan har Amurka ta ci gaba da kashe Al’ummar musulmin da basu ji basu gani ba.Ana saran yanke masa hukunci ranar 12 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.