Kenya

An yi garguwa da ma’aikatan agaji a Kenya

Jami'an agaji a sansanin 'yan gudun Hijira da ke Dadaab na kasar Kenya
Jami'an agaji a sansanin 'yan gudun Hijira da ke Dadaab na kasar Kenya REUTERS/Thomas Mukoya

Jami’an tsaro a kasar Kenya sun tabbatar da sace wasu jami’an agaji mata biyu 'yan kasar Spain a yankin Dadaab sansanin ‘yan gudun hijara a kasar Kenya. Kuma ana tunanin an yi garkuwa da su ne a kan iyakar kasar Somaliya.Jami’an tsaro sun tabbatar da jami’an da aka yi garkuwa da su ma’aikatan kungiyoyin agaji ne na kungiyar Doctors Without Borders, kuma ana zargin kungiyar Al Shabeb ce ta yi garkuwa dasu.Sansanin Dadaab shi ne sansanin ‘yan gudun Hijira mafi girma a duniya, wanda yanzu haka ke dauke da ‘yan gudun hijira 450,000 yawancinsu wadanda suka gudo ne daga kasar Somaliya saboda fama da matsanancin yunwa a kasar.