Libya

An tabbatar da mutuwar Khamis Gaddafi a Libya

Hoton Bidiyon Khamis dan Muammar Gaddafi
Hoton Bidiyon Khamis dan Muammar Gaddafi @Reuters

Kafar yada labaran Telebijin mai goyon bayan Gaddafi ta tabbatar da mutuwar Khamis Gaddafi, wanda aka ruwaito ‘yan Tawayen libya sun kashe a watan Ogusta.Kafar yada labaran Arrai ta kasar Syria dake yada sakwannin Gaddafi da manufofinsa ta sanar da cewa an kashe Khamis Gaddfi ne a ranar 29 ga watan Ogusta a yankin Tarhuna da ke nisan Mile 50 da kudu maso yammacin birnin Tripoli.An sanar da mutuwar Khamis Gaddafi ne tare da na hannun damar mahifinsa Abdullah al-Senussi.Wannan dai shi ne karo na farko da kafar yada labaran ta tabbatar da mutuwar Khamis wanda ake ta yayata mutuwarsa a kwanan baya.