Tunisiya

Shugaban rikon Tunisia ya yi alkawarin mika mulki

Masu kada Kuri'a a Tunisiya
Masu kada Kuri'a a Tunisiya REUTERS/Louafi Larbi

Watanni tara bayan zanga zangar da ta tumbuke gwamnatin Zine el Abidine Ben Ali, Shugaban rikon kasar Tunisia Foued Mebazaa ya ce zai mika mulki ga duk wanda majalisar dokokin kasar ta zaba. A yau ake zaben yan majalisar, kuma Alamu na nuna jama’iyyar masu kishin Islama ta Ennahda, za ta sami gagarumin rinjaye, a kuri’ar da mutane fiye da Miliyon 7 za su zabi ‘yan majalisa 217, da za su sake ruduta kundin tsarin mulkin kasar, da ke Arewacin nahiyar Africa. Majisar za ta zabi shugaban rikon da zai mulki kasar kafin a kammala tsara kundin mulkin, da za a yi cikin shekara daya.