Najeriya

Kungiyoyin Fararen hula zasu gudanar da zanga-zanga a Najeriya

Comrade shehu Sani shugaban kungiyar fararen hula ta Civil Right Watch
Comrade shehu Sani shugaban kungiyar fararen hula ta Civil Right Watch RFIHAUSA/Atayi

Kungiyoyin fararen hula a Nijeriya, sun shirya yin gangami a wasu sassan manyan biranen kasar don nuna bacin ransu da yadda Gwamnati ta kasa samar da wutar lantarki duk da makudan kudaden da take kashewa wajen gudanar da aiki a fannin. Kungiyar transparency Nigeria da zata jagoranci gangamin zasu gudanar da gangamin ne a biranen Abuja da Lagos da Port Harcout da kuma birnin London da New York na Amurka.A wata sanarwa da masu jagorantar gangamin suka aikawa manema labarai sun ce zanga-zanga ce ta lumana kuma bata da nasaba da wata Jam’iyyar Siyasa ko kuma wani guri na Siyasa. 

Talla

Shehu Sani Shugaban kungiyar Civil Right Congress

A cewarsu Gangamin zai shafi kira ga gwamnati tare da wayar da kan al’umma kan halin matsalar wutar lantarki da Nijeriya ke ciki da ya haramtawa kasar ci gaba wajen samun abubuwan more rayuwa.

Matasa a Najeriya na fama da matsalar aikin yi, ga matsalar tsaro da ke barazana ga rayuwar al’ummar kasar da rashin samun ingantaccen kiyon lafiya da Ilimi.

Shettima Yerima

Comrade Shetima Yarima na kungiyar matasan Arewa na daya daga cikin masu shirya zanga-zangar kuma yace matsalar wutar lantarki a Najeriya shi ya haifar da Talauci da fashi da makami da sauran matsaloli da suka durkusar da ci gaban Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.