Kenya-Somaliya

Somaliya ta fara adawa da kutsen Kenya cikin kasar

Shugaban Somalia Sheikh Sharif Sheikh Ahmed
Shugaban Somalia Sheikh Sharif Sheikh Ahmed REUTERS/Murad Sezer

Kasar Somaliya ta kalubalanci hurumin da kasar Kenya ke da shi na kai samame yankinta domin farautar Dakarun Al-Shabab, matakin da kasar Faransa ke goyon baya.Kasar Faransa dai ta fito fili tace Dakarun kasar Kenya su ci gaba da yaki cikin kasar Somaliya, tare alkalin bada taimakon kayan yaki ta sama.A cewar Shugaban kasar Somaliya Sharif Sheikh Ahmed, san ba zasu bari ba, mutan kasar su zuba idanu ayi masu kutse.Shugaban Somaliyan ya fadawa manema labarai a birnin Mogadishu cewa dangantakar da ke tsakaninsu da Kenya, it ace ta neman Sojan kasarsu da ke aikin horas da Sojan Somaliya amma ba wai ayi masu kutse ba.Kwanaki 8 kenan dai da Dakarun kasar Kenya suka fara dannawa yankin Somaliya, saboda zargin yadda wasu ‘yan kungiyar Shabab da ke Somaliya ke tsallakawa zuwa Kenya, suna sace ‘yan kasashen waje suna tserewa zuwa cikin kasar.Wannan matsayi na Shugaban kasar ya sabawa yarjejeniyar da Ministocin Tsaro na Kenya da Somaliya suka sanya wa hannu inda suke cewa sun amincewa wajen taimakawa juna ta fannin tsaro da ayyukan soja.