Libya

An yi Jana’izar Gaddafi a asirce a Libya

'Yan Tawayen Libya na murnan kisan Gaddafi da samun 'yancin Libya
'Yan Tawayen Libya na murnan kisan Gaddafi da samun 'yancin Libya REUTERS/Esam Al-Fetori

Hukumomin gwamnatin wuccin gadin Libya sun sanar da yin Jana’izar tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi a asirce, a wani kabarin da aka kebe a yankin Sahara domin kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan nuna gawarsa a bainar jama’a.A ranar Alhamis makon jiya ne  dakarun ‘yan tawaye suka kashe Gaddafi tare da girke gawarsa mutane na zuwa kallo inda  takaddama ta kaure akan yadda zasu yi da gawar tsohon shugaban da aka kwashe watanni ana yakin kawo karshen mulkinsa.Tun da farin dai gwamnatin wuccin gadi ta bukaci ‘yan kabilarsa a mahaifarsa a birnin Sirte wurin da suke ganin ya dace a binne tsohon shugaban domin kaucewa mayar da kabarinsa wajen Ibada.