Amurka-Niger-Code d'Ivoire-Guinea

Amurka ta daidaita huldarta da Nijar da Code d’Ivoire

Shugaban Amurka Barak Obama
Shugaban Amurka Barak Obama

Shugaba Barack Obama, ya mayar da kasashen Cote d’ivoire da Jamhuriyar Nijer da Guinea, a kan matsayinsu, na abokan kasuwanci da Amurka, saboda kasashen sun gudanar da karbabben zabe. Bayan nazarin kungiyar cinikayya tsakanin Amurka da kasashen Africa ta AGOA, shugaban ya sanar da mayar da kasashen a matsayinsu, a dai dai lokacin da yake shirin kama hanya zuwa kasar Faransa, don halartar taron kungiyar kasashen 20 masu karfin tattalin arziki a makon gobe.Tun shekaru biyar da suka gabata ne kasar Code d’Ivoire ke fuskantar barazana bayan barkewar rikicin siyasa a shekarar 2005.A bara Amurka ta sake kakubawa kasar Takunkumi bayan barkewar rikici da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3,000 bayan kammala zeban shugaban kasa a watan Nuwamba inda Laurent Gbagbo yaki amincewa ya sauka daga karagar mulki bayan ya sha kaye.A shekarar 2009 ne aka dakatar da kasar Jamuhuriyyar Nijar bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin farar hula ta Mamadou Tanja wanda ya yi yunkurin sauya kundin tsarin mulkin kasar domin bashi damar yin tazarce.A shekarar bara kasar Amurka ta shigo da kayayyaki daga Code d’Ivoire masu darajar kudi Dala Miliyan $163, kayayyaki kuma daga Guinea akan kudi dala Miliyan $85, daga Jamuhuriyyar Nijar kuma Amurka ta shigo da kayayyaki Dala Miliyan $50.