Nijar

Ana zaman makoki a Nijar bayan mutuwar tsohon shugaban kasa

Ali Saibou Tsohon shugaban Jamhuriyyar Nijar
Ali Saibou Tsohon shugaban Jamhuriyyar Nijar AFP

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar zaman makoki na kwanaki uku, saboda rasuwar Tsohon shugaban kasa, Janar Ali Saibou, wanda ya rasu jiya yana da shekaru 71. Gwamnatin kasar tace a gobe Laraba ne za'a yi Jana'izar tsohon shugaban.Tsohon shugaban ya jagoranci kasar da ga shekarar 1987 zuwa 1993, bayan rasuwar Janar Seini Kountche, inda ya dora ta a tirbar demokradiya, abinda ‘Yan kasar da duniya ke ci gaba da tuna shi akai.A shekara 1989, an zabi Janar Ali Saibou a matsayin shugaban kasa, da kuri’u sama da kashi 99, amma shekaru biyu bayan haka, sai ya kaddamar da taron kasa, abinda ya bude sabon babi a siyasar Jamhuriyar Niger, inda aka samu Jam’iyu da dama.Bayan saukarsa daga karagar mulki, Janar Ali Saibou ya kauracewa siyasa.Shugaban kasa Muhammadu Yusufu ya bayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar, inda za’a sauke tutocin kasar, yayin da ake gudanar da jana’izar sa a garin Dingajibanda. 

Talla

Ben Umar Muhammed

Shugabana Jam’iyar PNA Al’umma, Sanusi Tambari Jacku, ya yaba da rawar da Tsohon shugaban ya taka, wajen sake firsinonin siyasa, har ma da shi kansa, da kuma gina harsashin demokradiya.

Ben Umar Muhammed, Dan Majalisa a kasar, yace Afrika ba zata manta da rawar da Tsohon shugaban ya taka ba, wajen girka taron kasa, wanda ya shatawa kasar hanyar siyasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.