Libya-Nijar

An samu mutuwar mutane 14 bayan tawagar Libya ta ratsa Nijar

Wani soja rike da makami a kan iyakar Nijar da Libya
Wani soja rike da makami a kan iyakar Nijar da Libya AFP

Akalla mutane 14 aka tabbatar da mutuwarsu, a arangamar da aka yi tsakanin dakarun Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da wasu Yan bindiga da suka fito daga kasar Libya, kan hanyar zuwa Mali.Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin Dillancin labaran Reuters cewa, ‘Yan bindigan magoya bayan Tsohon shugaban Libya ne Muammar Gaddafi, da ke samun rakiyar Abzinawa, inda aka kashe 13 daga cikinsu, Sojan Nijar guda daya kuma ya mutu.Gwamnatin Niger tace sojin ta sun kwace bindigogi 36, masu sarrafa kansu 11, da makaman harba roka uku, da kuma harsasai 11,000.