Liberia

‘Yan adawa a Liberiya zasu gudanar da Zanga-zanga

Madugun adawa na Jam'iyyar CDC Winston Tubman, tare da magoya bayansa à Monrovia.
Madugun adawa na Jam'iyyar CDC Winston Tubman, tare da magoya bayansa à Monrovia. REUTERS/Finbarr O'Reilly

‘Yan Adawa a kasar Liberiya, sun yi kiran gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta kwanaki biyu, domin nuna juyayin wadanda suka mutu a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar. A yau litinin ne ‘yan adawar suka shirya yin jana’izar wadanda aka kashe kafin zabe, da kuma wadanda suka mutu bayan sake gudanar da zaben zagaye na biyu.Mataimakin kula da yakin neman zaben Jam’iyyar CDC, George Solo, yace suna tattaunawa da iyalan wadanda aka kashe don yi musu jana’iza.Shugaban Yan adawan Winston Tubman wanda ya kauracewa zaben zagaye na biyu ya bukaci rusa zaben da Sirleaf ta lashe tare da neman bukatar ganin sake gudanar da wani zaben cikin wata daya.