Benin-Vatican

Fafaroma zai kai ziyara Jamhuriyyar Benin

Fafaroma Benedict lokacin da ya kai wata ziyara a Berlin kasar Jamus
Fafaroma Benedict lokacin da ya kai wata ziyara a Berlin kasar Jamus REUTERS/Max Rossi

A yau Juma’a Fafaroma Benedict zai kai ziyara kasar Jamhuriyar Benin, ziyarar shi ta biyu a Nahiyar Africa.Dubun dubatar ‘yan kasar, da ma baki ne za su tarbi Paparoma, a ziyarar kwanaki 3, da zai kammala a ranar lahadi, inda za’a gudanar da wata addu’ar filin wasan babban birinin kasuwancin kasar, Cotonou .Benedict na bin sawun wanda ya gada, Paparoma John Paul, wanda ya ziyarci jamahuriyar Benin sau biyu, tare da kai ziyara a kasashen Africa 41.