Najeriya

Akwai sa hannun ‘Yan siyasa a rikicin Boko Haram a Najeriya inji SSS

Usman Zawahiri na kungiyar Boko Haram a Najeriya lokacin da yake amsa tambayoyi a Hedikwatar SSS
Usman Zawahiri na kungiyar Boko Haram a Najeriya lokacin da yake amsa tambayoyi a Hedikwatar SSS Sahara Reporters/MARILYN OGAR

Rundunar Tsaro ta SSS a Najeriya, ta gabatar da Ali Sanda Umar Konduga, da ake wa lakabi da Usman al Zawahiri, a cikin wadanda ta kama a Maiduguri, kuma ya shaida mata cewar, wasu ‘Yan Jam’iyyar PDP ne ke basu kudi don tayar da hankalin Gwamnatin Jihar.Konduga ya gayawa manema labarai cewa shi tsohon dalibin Muhammad Yusuf ne Shugaban kungiyar Boko Haram wanda jami’an tsaro suka kashe a rikicn Maidugurin zamanin mulkin marigayi Yar’Adua.A cewarsa sukan aika da sako ta wayar Salula domin gargadi ga manyan ‘yan siyasa. Cikin wadanda aka aikawa da sakon sun hada da Senato Sanusi Dagash da mai shari’a Sabo Adamu.Kakakin rundunar SSS Merilyn Oga, ta ce Zawahirin yana cikin ‘Yan kungiyar ECOMOG da ‘Yan siyasa ke amfani da su, kuma yana yi wa manyan ‘yan Siyasa aiki ne da suka hada da marigayi Ambasada Sanda Pindar, da kuma Senata Ali Ndume.A cewar Merilyn aikin su shi ne aikawa da sakon barazana ga Gwamnati. Kuma cikin wadanda suka fuskanci wannan barazanar sun hada da Sule Lamido Gwamnan Jahar Jigawa da Gwamnan Niger Babangida Aliyu da tsohon Shugaban kasa Cip Olusegun Obasanjo.Sai dai Gwamnan Niger Babangida Aliyu ya musanta aika masa da duk wani sakon barazana ta wayar Salula, 

Talla

Hussaini Munguno, Masanin Sha'anin tsaro a Najeriya.

Masu sharhi kan sha’anin tsaro a Najeriya suna ganin idan har aka bayyana sunayen ‘yan siyasa a matsayin wadanda ke hura wutar rikicin Boko Haram ya dace ace akwai kwararan hujjoji da zasu tabbatar da sa hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.