Cote d’ivoire

Jam’iyyar Gbagbo zata kauracewa zaben ‘Yan Majalisu a Code d’Ivoire

Shugaban Rikon kwarya na Jam'iyyar Laurent Gbagbo ta PFI Sylvain Miaka Ouretto. lokacin da yake sanar da matakin kauracewa zaben 'yan Majalisu
Shugaban Rikon kwarya na Jam'iyyar Laurent Gbagbo ta PFI Sylvain Miaka Ouretto. lokacin da yake sanar da matakin kauracewa zaben 'yan Majalisu Reuters/Thierry Gouegnon

‘Yan takara 1,182 ke neman kujerun Majalisar kasar Cote d’Ivoire 255, a zaben da ake shirin gudanarwa a kasar, yayin da Jam’iyar Tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo ta bayyana kauracewa zaben.Mataimakin shugaban hukumar zaben kasar, Yacouba Bamba, yace wasu ‘Yan Jam’iyyar Gbagbo sun yi rajista ne a matsayin ‘Yan takarar Indefenda.Miaka Oureto Shugaban Jam’iyyar Gbagbo ta PFI yace zasu kaurace zaben domin hasashen za’a yi magudi.A watan Aprilu ne aka cafke Laurent Gbagbo bayan kawo karshen rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000 a lokacin da ya ki amincewa ya mika mulki ga Alassane Ouattara bayan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Nuwamba.