Masar

Masu zanga-zanga a Masar sun yi watsi da tayin gwamnatin Sojin kasar

Motar daukar wadanda basu da lafiya a Dandalin Tahrir birnin Al kahira na Masa
Motar daukar wadanda basu da lafiya a Dandalin Tahrir birnin Al kahira na Masa Reuters/

Dubun dubatar masu zanga zanga ne ke ci gaba da mamaye dandalin Tahrir a birnin Al Kahira bayan watsi da tayin da gwamnatin Sojin kasar ta yin a gaggauta mika mulki ga farar Hula.

Talla

Bayan an kwashe kwanaki hudu ana dauki ba dadi tsakanin masu zanga-zangar da Jami’an tsaro, shugaban Majalisar sojin kasar Field Marshall Mohamed Hussein Tantawi yace zasu gaggauta gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yulin badi.

A cewarsa, basu da bukatar ci gaba da rike mulki ko kadan, amma jawabin nashi bai samu karbuwa ba ga masu zanga-zangar, wadanda yanzu haka ke dandalin Tahrir a birnin Al Kahira domin neman ganin Shugaban ya yi saukar gaggawa.

A ranar Litinin ne gwamnatin Sojin kasar ta shirya gudanar da zaben ‘Yan Majalisu, bayan Majalisar ministocin kasar ta yi murabus.

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin soji gaggauta gudanar da zaben shugaban kasa kafin kawo karshen dauki ba dadin da ake yi tsakaninsu da Jami’an tsaro.

Yanzu haka mutane 37 suka mutu a zanga-zangar, wasu da dama suka samu rauni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.