Gambiya

'Yan Adawan kasar Gambia, sun yi zargi magudi a zaben kasar

Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh Reuters

A yau ne Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ke neman sake zabensa bayan kwashe shekaru 17 yana shugabancin kasar, zaben da kungiyar kasashen Yammacin Africa ta ECOWAS tace zata kauracewa domin shirya magudi.

Talla

Kimanin ‘yan kasar 800,000 suka yanki Rejistar kada kuri’a a zaben da Shugaba Jammey zai kara da 'Yan Takara daga Jam'iyyun guda biyu.

Tuni dai masu sa ido a zaben suka bayyana alamun shugaban ne zai lashe zaben bayan kwashe tsawon shekaru 17 yana saman mulki inda ake zarginsa da keta hakkin ‘Yan adawa.

Kungiyar kasashen Yammacin Africa ECOWAS ta kalubalanci sahihancin zaben inda ta bayyana  kauracewa saboda babu gaskiya a shirye shiryen gudanar da zaben.

Dan takaran Shugaban kasar na Babbar Jamiyyar adawa a kasar Gambia Osainou Darboe ya koka gameda yadda aka sami dimbin Sojan na gadin wuraren zaben da akayi yau, dama dukkan titunan kasar, inda yake fadin cewa mataki ne na harzuka jamaa

Yayi zargin cewa Sojan kasar sunfi kowa yiwa Shugaban kasar yakin neman kuri'u, saboda haka babu adalci a zaben.

Shugaban kasar Yahya Jameh wanda yah au kujeran mulkin kasar a shekara ta 1994, lokacin yana da shekaru 29, yana mulkin kasar ce da karfin tuwo.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.