Za a kawo Shugaban Guinea-Bissau jinya a Faransa
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Guinea-Bissau Malam Bacai Sanha, na sibiti ba lafiya, a kasar Senegal , kuma ana ganin za a tattarashi zuwa nan Paris domin ayi masa magani sosai.Wata sanarwa daga ofishin Shugaban kasar na cewa duba lafiyar tasa kawai za ayi kamar yadda ya saba, kuma zai zo wani asibitin Soja na Paris, mai suna Val de Grace, inda aka saba kwantar da Shugabannin kasashen Africa renon Faransa.Dan shekaru 64, Shugaban kasar Guinea Bissau tutur yakan tafi wannan asibiti, koda yake an ki fadi takamaiman cutar da yake fama da ita.