An fara kada kuri’ar zaben farko a Masar bayan hambarar da Mubarak
Wallafawa ranar:
Yau Al’ummomin kasar Masar ke kada kuri’ar zaben ‘Yan Majalisu, a wani yanayin rudani, sakamakon ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin riko ta Soji, zabe na farko kuma bayan Hambarar da Hosni Mubarak.
Shugaban sojin kasar, Field Marshall Hussein Tantawi, ya bukaci ‘Yan kasar fitowa kada kuri’ar su, inda ya yi gargadin cewar, ba zasu bari wani, ko wata kungiya ta kawo musu cikas kan shirin mayar da kasar turbar demokradiya ba.
Saeed Inuwa Ibrahim, Malami a Jami’ar Al Azhar.
Saeed Inuwa Ibrahim, Malami a Jami’ar Al Azhar, yace wasu ‘Yan kasar sun gaji da zanga-zangar, kuma sun fara nadamar korar shugaba Hosni Mubarak.
Wannan zaben shi ne na farko a jadawalin zabukan kasar da za’a ci gaba da gudanarwa har zuwa Watan Mayun badi.
An kwashe tsawon kwanaki 9 ana zanga-zanga adawa da gwamnatin Soji wadanda suka karbi mulki bayan hambarar da Hosni Mubarak wanda aka kwashe watanni ana zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.
Yanzu haka akalla mutane 41 ne aka kashe a sabuwar zanga-zangar, wasu da dama kuma suka ji rauni.
Wasu ‘yan kasar da dama sun yi barazanar kauracewa zaben ‘yan Majalisun inda suke ci gaba da kiran lalle sai gwamnatin Sojin kasar ta yi murabus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu