Jamhuriyyar Congo

An fara kada kuri’ar zaben shugaban kasa a kasar Congo

Lokacin wata arangama da jami'an tsaro a  Kinshasa.
Lokacin wata arangama da jami'an tsaro a Kinshasa. AFP PHOTO/Gwenn DUBORTHOMIEU

A yau al’ummar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo zasu kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘Yan majalisu sai dai rikici ya barke a jibirin zaben, inda mutane biyu suka mutu. Tun da karfe 6:00 na safe ne aka bude runfunan zabe.

Talla

A ranar assabar aka fara samun matsala, bayan da aka yi fito na fito tsakanin magoya bayan shugaba Joseph kabila da na madugun ‘yan adawa Etienne Tshisekedi, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan a kalla mutane biyu.

Magoya bayan Tshisekedi sun yi fito-na-fito da jami’an tsaro kusa da filin jirgin saman birnin Kinshasa, inda aka yi amfani da hayaki mai sa hawaye, da ruwan zafi da harsasai kafin tarwatsa gungun, inda a nan ma aka kashe mutun daya.

Tuni dai, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI, Ngoy Mulunda, ya shaida wa manema labaru cewa, za a gudanar da zaben na yau, kuma za a bude runfunan zabe kan lokaci.

Sakatare janar na Majalisar Dunkin Duniya Ban Ki Moon, ya yi kiran da a kai zuciya nesa, amma Tshisekedi ya nemi Moon ya gaggauta sauke Roger Meece shugaban rundunar wanzar da zaman lafiyan Majalisar a kasar, dan kasar Amurka, domin shakuwar Meece da shugaba kabila fiye da kima.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.