Jamhuriyyar Congo

An fara kidayar kuri’a a zaben kasar Congo

Wani yana kada Kuri'ar shi a wata mazaba a Kinshasha
Wani yana kada Kuri'ar shi a wata mazaba a Kinshasha Reuters/Finbarr O'Reilly

Jami’an gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun fara kidayar kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa, bayan barkewar rikici da zargin magudi a zaben.

Talla

Shugaba Joseph Kabila ya fafata ne da ‘Yan takara goma karkashin jagorancin madugun adawa Etienne Tshisekedi. Kimanin ‘Yan Takara 18,500 ne kuma ke neman kujerun Majalisar kasar 500.

A ranar 6 ga watan Disemba ne ake dakun sakamakon zaben.

An samu matsalar kai kayan aiki a wasu mazabu, inda hukumar zaben kasar ta bukaci wasu mazabun yin hakuri har zuwa ranar Talata domin kada kuri’arsu.

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wata mazaba a yankin Katanga. Kuma an samu barkewar rikici da magudi a sassan yankunan kasar.

Wannan shi ne zabe na biyu tun bayan yakin basasa a cikin kasar bayan gudanar da na farko a shekarar 2006.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.