Cote d’ivoire-ICC

Gbagbo zai gurfana gaban kotun duniya ta ICC

Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo wanda zai gurfana gaban kotun duniya ta ICC bisa zargin aikata laifukan yaki da fyade
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo wanda zai gurfana gaban kotun duniya ta ICC bisa zargin aikata laifukan yaki da fyade Reuters

A yau ne ake saran bude shari’ar Tsohon shugaban kasar Cote’dIvoire, Laurent Gbagbo, a kotun hukunta manyan laifufuka, wadda ke tuhumar sad a laifin kisa da fyade. A makon jiya ne aka mika Laurent Gbagbo zuwa Hague domin gurfana gaban kotu bisa zargin aikta laifukan yaki da fyde a rikicin siyasar da ya biyo bayan zabn shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamban bara inda ya ki amincewarsa ya mika mulki ga Ouattara bayan ya sha kaye a zaben.

Talla

Ana sa ran fara sauraren karar da karfe 1:00 agogon GMT inda alkalin kotun zai diba zarge-zargen da ake wa tsohon shugaban.

Ana zargin Gbagbo ne da aikata laifuka hudu da suka hada da kisa da Fyade da keta hakkin bil’adama, da dakarunsa suka aikata da umurninsa tsakanin watan Desembar bara zuwa watan Afrilun bana.

A ranar 23 ga watan Nuwamba ne kotun ICC ta bada sammacin kama tsohon shugaban.

Babban mai gabatar da kara a kotun Luis Moreno-Ocampo yace Gbagbo shi ne shugaba na farko da zai gurfana gaban kotun amma yace wasu shugabannin zasu bi sahunsa.

Kotun tana zargin shugaban kasar sudan Omar Hassan al Bashir da aikata laifukan yaki a rikicin yankin Darfur, da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da shugaban kasar Chadi Idris Derby. Matakin da wasu suke ganin kotun ta sa ido ne ga shugabannin kasashen Afrika.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI