Cote d’Ivoire

An fara samun Sakamakon zaben 'yan Majalisun kasar Cote d"ivoire

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara REUTERS/Luc Gnago

Rahotanni daga kasar Cote d’Ivoire na cewa jam'iyyar Shugaban kasar Alassane Ouattara na kan gaba wajen kuri'u, a zaben wakilan majalisar kasar. Har ya zuwa dazun nan dai ana ta karkare kidaya kuri'un zaben.

Talla

Ya zuwa dazun alkaluman zaben na nuna cewa daga cikin kujeru 255, jam'iyyar ta sami kujeru 123 yayin da jamiyyar Ivory Coast Democratic Party, PDCI, ta samu 93.

Kungiyar ECOWAS-CEDEOA ta YAmmacin Afrika, ta ce zaben wakilan majalisar kasar ta Cote d’Ivoire da aka yi karshen makon gabata anyi adalci kuma babu wata kunbuya-kunbuya.

Wakilan kungiyar ta ECOWAS da suka sa idanu kan zaben, sun fadi cikin wata sanarwa dazun nan cewa duk da cewa ba a rasa wasu kurakurai, amma zaben babu laifi sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI