Tunisia

An Rantsar da Sabon Shugaban Kasar Tunisia Marzouki

Sabon Shugaban Tunisia Moncef Marzouki
Sabon Shugaban Tunisia Moncef Marzouki Reuters/Zoubeir Souissi

Yau aka yi bikin rantsar da sabon shugaban kasar Tunisia, Moncef Marzouki, wanda ya zama shugaba na farko tun bayan juyin juya halin kasar. Yayin da yake rantsuwar kama aiki, sabon shugaban kasar, Marzouki, ya yi alkawarin kare martabar 'yan kasar da muradun ta, tare da kundin tsarin mulki.

Talla

Shugaban ya kuma yi alkawarin kare muradun wadanda suka rasa rayukansu a juyin juya halin kasar, inda ya ce duniya na kallon Tunisia a matsayin wani mizanin gwada demokradiya, tun bayan kifar da Gwamnatin shugaba Zine el Abidine ben Ali a farkon wannan shekara ta 2011.

Sabon Shugaban Tunisia Moncef Marzouki yayin rantsuwar kama aiki
Sabon Shugaban Tunisia Moncef Marzouki yayin rantsuwar kama aiki REUTERS/Zoubeir Souissi

Marzouki wanda ya zubar da hawaye yayin rantsuwar, ya ce zasu kambama al’adunsu na Larabawa Musulmi, kare martabar mata masu sa hijiba, da 'yan matan dake sanye da niqabi, da ma wadanda basa sanye da shi.

Sabon shugaban Moncef Marzouki mai shekaru 66, ya kwashe shekaru da dama yana gudun hijira a kasashen waje, kafin kauda gwamnatin Ben Ali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI