Najeriya

‘Yan Sandan Najeriya sun cafke muh’d Hamza da ake zargin dan Boko Haram ne

Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya  Hafiz Ringin
Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya Hafiz Ringin Nigerian Leadership

‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke Muhammed Hamza daya daga cikin shugabannin kungiyar Boko Haram, bayan musayar wuta a birnin Kano da ke arewacin kasar.‘Yan sandan sun ce sun cafke shi ne lokacin da yake kokarin ficewa daga cikin birnin bayar musayar albarussai a harabar gidansa.

Talla

A cewar shugaban rundunar ‘Yan sandan Jahar Ibrahim Idris, ‘Yan sanda hudu sun gamu da ajalinsu.

A ranar Alhamis ne wasu da ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari a wata makarantar Sakandare ta ‘Ya'yan Sojoji, inda suka kashe Sojin sama hudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI