Jamhuriyyar Congo

An haramtawa Tshisekedi rantsar da kansa Matsayin shugaban kasa a Congo

Etienne Tshisekedi, Madugun adawar Jamhuriyyar Congo
Etienne Tshisekedi, Madugun adawar Jamhuriyyar Congo REUTERS/Finbarr O'Reilly

Rundunar ‘Yan sandan kasar Jamhuriyyar Congo ta haramtawa Madugun adawar kasar, Etienne Tshisekedi gudanar da bukin ratsar da shi bayan kin amincewa da sake zaben Joseph Kabila matsayin Sabon shugaban kasa.  

Talla

Rundunar ‘Yan sanda tace akwai shugaban kasa wanda aka rantsar a cikin kasar, don haka ba zasu amince da wani bukin rantsuwa ba.

Tuni dai Shugaban kasar Joseph Kabila ya yi rantsuwar zarcewa da mulkin kasar bayan an bayar da sakamakon zabe wanda bangaren ‘yan adawa ke cewa shirme ne.

A halin da ake ciki dai Hukumar zaben kasar tace ta tsayar da kidayar kuri’un zaben wakilan majalisar kasar, sakamakon zargin magudi.

‘Yan takara 18,000 suka tsaya takara domin neman kujeru 500 a majalisar wakilan kasar.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.