Masar

Mubarak ya sake gurfana gaban kotu bayan watanni uku

Wani mai adawa da Hosni Mubarak yana kone hoton shugaban
Wani mai adawa da Hosni Mubarak yana kone hoton shugaban REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

A yau laraba ne tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya sake gurfana gaban kotu bayan dage sauraren kararsa watanni uku da suka gabata. Mubarak zai fuskanci hukuncin Kisa bisa zarginsa da kisan masu gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.

Talla

Kafar Telebijin din kasar ta nuna hoton tsohon shugaban mai fama da rashin lafiya kwance sanye da fararen tufafi a lullube da bargo.

Hosni Mubarak wanda ke tsare a Asibitin sojoji a birnin Alkahira, ana zarginsa ne da bada umurnin kisan mutane 850 wadanda suka mutu a lokacin zanga-zangar da ta yi sanadiyar kawo karshen mulkinsa a watan Fabrairu.

‘Yan sanda kimanin 5,000 ne suka kewaye harabar kotun da ake sauraren karar tsohon shugaban.

Yanzu haka kuma ‘Yayan Tsohon shugaban guda biyu Alaa da Gamal dukkaninsu sun bayyana a gaban kotun tare da tsohon ministan cikin gida Habib al-Adly da ake zargi da kisan masu zanga-zanga.

Idan dai har aka kama Mubarak da laifi zai fuskanci hukuncin kisa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI