kudancin Sudan

Dubban mutane ne ke cikin wani hali a Kudancin Sudan

Valerie Amos
Valerie Amos

Dubban mutane ne ke cikin wani hali a kasar Kudancin Sudan , sakamakon kazamin fadan kabilanci da ya kaure, a jihar Kudancin Kordofan, kamar yadda Shugaban Komitin jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos, ke cewa.Bayan ta tattauna da jamian Gwamnati a Khartoun, ta fadi cewa ‘yan gudun hijira dake Habasha da kudancin Sudan sun babbayana matukar bukatar kayan abinci da sauran muhimman bukatu a matsugunan da suke.Saidai kuma Ministan Kyautata jindadin jama'a na kasar Sudan Amira al-Fadel tace Hukumomin Gwamnatin kasar ne zasu raba kayan agajin da aka samu daga Majalisar Dinkin Duniya ga mabukata.