Libya

An bukaci gwamnatin Libya samar da mafita ga ‘Yantawaye

Tsohon mataimakin Fira Ministan kasar Libyar Ali Tarhouni lokacin yake ganawa da manema labarai a birnin Tripoli
Tsohon mataimakin Fira Ministan kasar Libyar Ali Tarhouni lokacin yake ganawa da manema labarai a birnin Tripoli Reuters路透社

Tsohon mataimakin Fira Ministan rikon kwaryan kasar Libya, yace dole hukumomin kasar su samar wa ‘Yantawayen kasar wata makoma, maimakon ci gaba da rike da muggan makamai.Ali Tarhouni, mai bai wa gwamanti mai ci shawara yace, in har ba a gaggauta yin hakan ba, za’a ci gaba da samun tashe tashen hankula a cikin kasar. 

Talla

Rikicin Kasar Libya
Tutar Kasar Libya

Tarhouni wanda ke Magana a birnin Washington a kasar Amurka, yace dole a dora mayakan kan wata turbar da zasu amince da ita, amma ba ci gaba da daukar makamai ba.

Ya kara da cewa dole a duba bukatunsu, da suka hada da horaswa da ilmantarwa, tare da kula da lafiyarsu, domin da dama daga cikinsu suna da burin komawa gudanar da rayuwarsu yadda suka saba a baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI