Afrika ta Kudu

Jam’iyyar ANC ta yi bukin cika shekaru 100 a Afrika ta kudu

Shugaban kasar Afrika ta kudu  Jacob Zuma, Lokacin da yake gabatar da jawabi a bukin cika shekaru 100 na jam'iyyarsu  ta ANC
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, Lokacin da yake gabatar da jawabi a bukin cika shekaru 100 na jam'iyyarsu ta ANC REUTERS/Siphiwe Sibeko

Jam’iyyar ANC a kasar Afrika ta kudu, ta yi bikin cika shekaru 100 da kafuwa, inda shugaba Jacob Zuma, ya yaba da rawar da kungiyoyin ma’aikata, maza da mata da, matasa, da bangarori dabam dabam suka taka, wajen kwatar ‘yanci, da kuma gina kasa, a gagarumin bikin da ya tara dubban mutane daga sassan duniya dabam dabam.

Talla

Tsohon Dan takaran shugabancin Amurka, kuma mai fafutukar ‘Yantar da bakaken fata, Rev Jesse Jackson, yace har yanzu akwai aiki a gaban Jam’iyar.

A cewarsa suna alfahari da ANC, amma akwai aiki a gabanta, domin kawo karshen nuna wariyar launin fata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI