Najeriya

Kiristoci zasu kare kansu, Jonathan yace akwai ‘Yan Boko Haram a gwamnati

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, yace akwai Jami’an Gwamnati da ‘Yan Majalisu, da bangaren shari’a da ke da alaka da kungiyar Boko Haram bayan kungiyar kiristocin kasar ta bukaci mabiyanta kare kansu tare da zargin shugabannin Musulmi a Arewacin kasar da ake kai hare hare.

Talla

Mista Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen addu’ar tunawa da mazan jiya. A cewar shugaban akwai wakilan kungiyar Boko Haram cikin jami’an tsaro.

Kalaman shugaban na zuwa ne bayan kungiyar kiristocin kasar karkashin jagorancin Ayo Orisajefe sun nemi mabiyansu kare kansu tare da rashin nuna gamsuwa da shugabannin musulmi da gwamnonin arewa na rashin daukar mataki game da hare haren da ake kai masu.

Dr Khalid Aliyu Sakataren kungiyar Musulmi ta Jama’atul Nasril Islam

An samu hare hare a sassan yankunan arewacin Najeriya inda kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai hare haren.

Amma Dr Khalid Aliyu Sakataren kungiyar Musulmi ta Jama’atul Nasril Islam yace shugaban kiristocin yana neman tashin hanakali ne a kasar tare da shafa kashin kaji ga al’ummar Masulmi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI