Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bukaci ma’aikata komawa aikinsu ko ta haramta masu albashi

A birnin Abuja, Kiristoci sun yi kawanya ga al'ummar musulmi dake gudanar da ibada a dandalin Zanga-zanga.
A birnin Abuja, Kiristoci sun yi kawanya ga al'ummar musulmi dake gudanar da ibada a dandalin Zanga-zanga. © Reuters/Afolabi Sodtunde

An shiga kwanaki uku na yajin aikin ma'aikata a Najeriya yayin da gwamnatin Tarayya ta bada umurni ga ma’aikatan kasar komawa ga aikinsu ko kuma ta dauki matakin haramta masu albashi.Wannan sanarwar ta fito ne daga Ministan shari’a Muhammad Adoke, wanda yace ya zama dole ma’aikata su yi la’akari da yarjejeniyar da suka kulla da ma’akatarsu idan kuma suka bijere zasu dauki matakin haramta masu albashi.

Talla

Yajin aikin wanda aka fara a farkon makon nan, ya durkusar da tattalin arzikin Najeriya a dai dai lokacin da gwamnatin Jonathan ke cikin mawuyacin halin matsalar tsaro.

Hotunan Zanga-zanga a Legas

Masana tattalin arziki sun ce yajin aikin a Najeriya da rikicin kasashen Yammaci da Iran ya haifar da hauhawan farashin Mai a duniya.

Gwamnatin kasar ta yi kiran kungiyoyin kwadago domin janye yajin aikin karkashin umurnin kotun masana’antu.

Ngozi Okonjo-Iweala da ake zargin kitsa janyen Tallafin ta nisanta kanta daga tilastawa Gwamnati amincewa da shirin, inda ta daura alhakin ga Gwamnonin kasar wadanda suka bai wa Gwamnati shawarar cire tallfin, watanni shida kafin ta karbi aikin Minista.

 

Yanzu haka kuma kungiyar kwadago tace babu gudu babu ja da baya domin zata ci gaba da yajin aikin har sai gwamnatin ta sauya matsayinta.

Hafiz Ringim Sufeto na 'Yan sandan Najeriya

An samu mutuwar mutane da dama amma jami’an tsaron kasar sun ce mutane shida ne suka mutu.

Wasu ‘Yan bindiga a Jahar Edo, sun kai hari kan Musulmi, inda suka kashe mutane biyar, suka kuma kona musu Masallaci.

A Jahar Lagos wasu Zauna garin banza, da aka fi sani da sunan Area Boys, sun kai hari ga wakilin Muryar Amurka, Ladan Ibrahim Ayawa, inda suka masa duka, kuma suka kwace kayan aikinsa.

Ladan Ayawa Wakilin muryar Amurka

Gwamnatin Jahar Kaduna, ta sanya dokar hana fita na sa’oi 24, abinda ya kawo adadin Jihohi uku da suka takaita zirga-zirgan mutane, saboda zanga zangar da ake yi, bayan Jihohin Kano da Zamfara.

A jiya Talata Shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya gana da manyan jami’an tsaron kasar, bayan kwashe kwanaki biyu ana yajin aiki da zanga-zanga, saboda daukar matakan da suka dace don kaucewa rikidewar zanga-zangar zuwa rikicin addini da kabilanci.

Rahotanni a kasar sun ce, ‘Yan Sanda sun kashe mutane 11 a sassan kasar daban dabam, amma Sufeto Janar, Hafiz Ringim yace jita jita ne.

Cikin wannan hali da ake ciki a Najeriya, Sakatare Janar na Majalisar Dikin Duniya Ban Ki-moon ya gana da Ministan harakokin wajen kasar Olugbenga Ashiru saboda fargabar da Majalisar ke nunawa game da tashin hankali a kasar.

Wannan ganawar na zuwa ne bayan wani rehoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar cewa, Kungiyar Boko Haram da ake zargin kaddamar da hare hare a Najeriya tana da hannu da kungiyar Al Qaeda.

Masana sha’anin tsaro suna danganta yiyuwar ballewar yakin basasa a Najeriya idan har hukumomin kasar basu dauki mataki ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI