MDD ta bukaci gudanar da karbabben zabe a Senegal
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kiran gudanar da karbaben zaben shugaban kasar Senegal da za’a yi a watan gobe, kamar yadda Jakadan Majalisar Said Djinit, ya bukaci daukacin ‘Yan Takarar hada kansu domin samun nasara.
Gobe ne ake saran kotun da ke Fassara kundin tsarin mulkin kasar, zata yanke hukunci game da takarar shugaba Wade, mai neman wa’adi na uku.
Sai dai Yossou Ndour, fitaccen mawaki kuma Dan takarar shugaban kasa, ya bukaci kasashen duniya hana shugaba Wade takara.
A cewarsa Mista Wade, ba shi da hurumin takara, domin zai jefa kasar ne cikin tashin hankali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu