Algeriya

An gwabza fada tsakanin 'yan sanda da matasa a Algeriya

CIA

A kasar Algeria mutane akalla 30 suka sami munanan raunuka ciki har da dan-sanda, sakamakon kazamin fadan daya kaure a wajen janaizar wani mutun daya babbaka kansa ya kone kurmus.Haka kawai mutumin mai suna Hichem Gacem, wanda ke sana’ar saida tabarau na idanu, ya watsa fetur a jikin shi, ya babbaka kansa a kauyen su dake Tiaret kilomita 340 yammacin birnin Algiers.Wannan alamari dai ya harzuka matasa dake wasu yankunan kasar dake zargin ‘yan sanda suka uzurawa matashin, suka shiga rufe hanyoyi da farautar ‘yan sanda ana fada dasu.