Congo-Brazzaville

Fashewar makamai ta hallaka mutane 150 a Brazzaville na Congo

AFP/Guy-Gervais Kitina

Akalla mutane 150 aka tabbatar da mutuwar su a hadarin da aka samu a tashar aje makaman dake Brazzaville babban birnin kasar Congo.Wani jami’in diplomasiyar kasar Faransa, ya shaidawa kanfanin Dillancin labaran kasar cewar, sun kirga gawawaki 150 a asibitin sojin Brazzaville, yayin da sama da mutane 1,500 suka samu raunuka.Rahotanni sun ce, yawancin wadanda suk asamu raunukan sojoji ne. 

Talla

Hukumin kasar Congo Brazzaville, sun tabbatar da kazancewar lamarin, sakamakon wata fashewar da aka samu, a ma’ajiyar makaman kasar.

Betu Bangana, jami’in hulda da jama’a a fadar shugaban kasa, ya ce majiyar asibiti ta tabbatar musu da adadin, yayin da wasu mutane da dama suka makalle a burabuzan gine gine.

Tunda fari, Ministan tsaron kasar, Charles Zacharie Bowao, ya yi watsi da rade radin juyin mulki, inda ya ce wuta ce ta haifar da hadarin.

Rahotanni sun ce karar fashewar sun fasa tagogi a makwaciyar kasar, wadda kogi ya raba su, wato kasar janhuriyar Demokaradiyar Congo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.