‘Yan adawar Senegal sun hade kai domin haramtawa Wade yin Tazarce
Wallafawa ranar:
Gamayyar ‘Yan adawar kasar Senegal sun hade kai tare da gudanar da wani gangami domin haramtawa shugaba Abdoulaye Wade mai shekaru 85 yin tazarce wa’adi na uku inda zasu marawa Macky Sall abokin hamayyarsa baya a zaben shugaban kasa zagaye na biyu.
‘Yan takarar shugaban kasa 12 wadanda suka fice takarar zabe a zagayen farko da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairu sun hada kawance ne domin tabbatar da tsohon Fira Ministan kasar Mista Sally a kai ga nasara.
Wannan kuma ke nuna cewa Wade yana fuskantar barazana a zaben zagaye na biyu da za’a gudanar a ranar 25 ga watan Mayu
A ranar Lahadi ne ‘yan adawar kasar zasu gudanar da wani gangami a dandalin Obisek cibiyar zanga-zangar adawa da tazarcen Wade.
Tsawon shekaru 12 ne Abdoulaye Wade ya kwashe yana shugabancin Senegal, kuma yanzu yana neman zake zabensa karo na uku bayan kammala wa’adi na biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya bashi dama.
Kasashen Amurka da Faransa sun bukaci Abdoulaye Wade yin Ritaya amma shugaban ya yi watsi da bukatarsu tare da yin biris da zanga-zangar da al’ummar Senegal ke gudanarwa domin nuna adawa da tazarcen shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu