Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Sandan Najeriya sun haramta shiga da mota a wuraren ibada a Plateau

Jami'an tsaro lokacin da suke kokarin kwantar da mutane bayan kai harin Bom a majami'ar St. Finbarr's Catholic a garin Jos
Jami'an tsaro lokacin da suke kokarin kwantar da mutane bayan kai harin Bom a majami'ar St. Finbarr's Catholic a garin Jos Reuters / Stringer
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Jami’an tsaro da jami’an gwamnati da shugabannin Addini a Jahar Plateau sun gana a jiya Talata inda suka amince da matakan shawo kan matsalar hare haren bama bamai da kunar bakin wake da ake kai wa a Jahar musamman birnin Jos wanda ya yi fama da tashin hankali.

Talla

Tattaunawar da aka gudanar a hedikwatar ‘Yan Sandan Jahar, shugabanin da suka halarci taron sun bukaci samar da hanyoyin magance matsalar tsaro a Jahar.

Reheton Tasiu Zakari daga Jos

Kwamishinan ‘Yan sandan Jahar Emmanuel Ayeni, wanda ya yi jawabi a taron yace daga yanzu za’a haramtawa mutane shigar da motocinsu a harabar wuraren ibada tare da kiran shugabannin addini amincewa da wannan matakin.

 Yanzu haka kuma duk motar da zata shiga wurin hada hadar Jama’a sai an bincike ta ciki da waje. Kuma kwamishinan ya yi kira ga al’ummar Jahar Plateau domin ba ‘Yan Sandan Jahar goyon baya don kaucewa tashin bama bamai a Jahar.

 

An dai dade ana rikici a garin Jos na kabilanci da Addini, kuma yanzu matsalar tsaro ce ke addabar Jahohin Arewacin Najeriya inda ake alakanta hare haren bama bamai da kungiyar da ake Kira Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.