Najeriya

Mutane bakwai ke fuskanci tuhuma kan awun gaba da kudaden Fansho

REUTERS/Akintunde Akinleye

Mutane Bakwai ne ake saran zasu gurfana a gaban kotu a Tarayyar Najeriya, saboda sace naira bilyan 14, kudin fanshon 'Yan Sandan kasar.

Talla

Mutanen sun hada da Abubakar Kigo, Babban Sakataren ma’aikatar Niger Delta, Esias Dangabar, Darakta a Hukumar Fanshon Yan Sanda, mukaddashin kwamishina 'yan Sanda, Okafor, da mataimakin Darakta, Ahmed Wada, wanda yanzu ke ma’aikatar wasanni a matsayin Darakta, kana kuma da Abdullahi Umar, mataimakin Darakta a ma’aikatar aiyuka.

Sauran sun hada da John Yusuf da Vickey, wadanda akawun kudade ne a ofishin fansho.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.